Gwamnatin Kano ta sanar da ranar komawa makarantun Boko
Daga Shafaatu Dauda Kano
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ranar komawa makarantun Firamare da Sakandare domin ci-gaba da ɗaukar karatun zango na uku na shekarar 2024/2025.
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ce ta sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar inda ya ce komawa makarantar ta shafi makarantun gwamnati da kuma masu zaman kansu.
A cewar Balarabe Ƙiru, “Ɗaliban makarantun kwana zasu koma a ranar Lahadi 6 ga watan Afirilun shekarar 2025, a inda ɗaliban jeka ka dawo zasu koma ranar litinin 7 ga wata, adan haka muna fatan iyaye za su kiyaye da wannan sanarwa”.
KU KUMA KARANTA:Ba za mu sauya tsarinmu na rufe makarantu a watan Azumi ba – Gwamnonin Kano, Bauchi, da Kebbi
Haka kuma Kwamishinan Ilimi na jihar, Gwani Ali Haruna
Makoɗa, ya gargaɗi dalibai kan komawa makarantun ɗauke da abubuwa da aka hana zuwa dasu kamar Reza, Wuƙa ko kuma kayan sanya maye.
Bugu da ƙari ya kuma nemi Malaman makarantun da su riƙe aikinsu tsakani da Allah sannan su koma aiki daga ranakun da aka tsara.
A ƙarshe kwamishinan ya bada tabbacin cewa gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusif, tana iya ƙoƙarin ta wajen haɓɓaka harkokin ilimi.