Gwamnatin Kano ta rufe wasu rumfuna

0
133
Gwamnatin Kano ta rufe wasu rumfuna

Gwamnatin Kano ta rufe wasu rumfuna

Daga Shafaatu Dauda Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta Rufe wasu Rumfunan adana kaya guda biyu a unguwar Sabon Gari dake karamar hukumar fagge bisalaifin keta ‘ka’idojin tsaftar muhali ta hanyar gurbata yanayi

Wata sanarwa da Daraktan wayar da Kan jama’a na ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi Isma’il Garba Gwammaja ya fitar a Ranar Asabar ce ta bayyana hakan.

Sanarwar tace, Rumfunan ajiyar dake hanyar filin jirgin Sama da ke kan titin Faransa,an gano cewa suna ajiye kayan kashe kwari da hayaki dake fitar da muggan wari,lamarin da ke damun ma zauna Yankin da masu wucewa ta wajen.

Daraktan Hana gurbatar muhalli a ma’aikatar,Malam Ibrahim Nasir,Wanda ya jagoranci gudanar da aikin,yace matakin ya Biyo bayan korafe-korafen da jama’a suke yi kan warin da ke fitowa daga ma’ajiyar.

KU KUMA KARANTA: Matsalar ruwan sha a Warawa ta jihar Kano, har ya kai ga suna shan ruwan da Karnuka ke Wanka

Bayan Samun koke-koken,sai muka Tura Jami’an Kula da muhalli domin gudanar da bincike,sakamakon binciken ya Tabbatar da Zargin,Kuma an aika da sanarwar ragewa ma’aikatan wajen ajiyar,Inda aka umarcesu dasuyi gaggawar kwashe kayayyakin,Rashin bin Umarnin da suka yi yasa aka Rufe harabar Kuma an Fara daukar matakin sharia inji Nasir.

Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi,Dakta Dahiru M.Hashim ya jaddada kudirin gwamnati na Kiyaye lafiyar Al’umma.

Dr.Hashim yace Ajiye Abubuwa masu hadari a wuraren Zaman al’umma Yana iya haifar da hadari GA muhalli da lafiya.

Ya Kuma ja hankalin mazauna Yankin da su Kai rahota ga hukumomin da suka dace,Inda ya kara da cewa ma’aikatar Zata ci gaba da zage damtse wajen Kare muhalli da bunkasar lafiya a Jihar Kano

Leave a Reply