Gwamnatin Kano ta rufe wani Otel bisa zargin yawaitar aikata baɗala
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnatin jihar Kano ta rufe gidan saukar baƙi na Fresco Guest Palace da ke Kumantaka a yankin Jaba na Karamar Hukumar Ungogo.
Shugaban Hukumar Yawon Bude Ido ta jihar Kano Alh. Tukur Bala Sagagi ne ya tabbatar da hakan ga Arewa Updates.
Ya ce, matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da suka samu na zargin lalata ƴan mata a Kumantakan, don haka jamiʼansu suka bibiya inda suka bankaɗo yadda ake kai ƴan mata ƙanana daga yankunan Birget, Tudunwada, Kwanar Jaba da kuma cikin Ungogo ana lalata da su.
KU KUMA KARANTA: Hukumar NSCDC a Legas, ta kama masu safarar mutane a wani otel
Hukumar ta kuma jagoranci rufe wasu wuraren shaƙatawa a unguwar Sabon Gari saboda rashin yin rajista, da kuma wanda aka rufe saboda samun su da tara ƴan mata ana mashaʼa.
Shugaban Hukumar ya gargaɗi dukkannin masu harkokin na gidajen yawon buɗe ido da shakatawa da su tabbatar sun kiyaye dokokin Kano da kula da tarbiyya da alʼada.









