Gwamnatin Kano ta kafa kotunan tafi da gidanka domin magance satar waya

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da kafa kotunan tafi da gidanka domin tabbatar da hukunta masu satar waya a jihar Kano cikin gaggawa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa ya fitar, ta ce kotunan tafi da gidanka za su yi aiki tare da rundunar haɗin gwiwa ta musamman domin hukunta waɗanda ake tuhuma.

Gwamna Abba ya ce manyan titunan birnin sun haska ne bayan shafe shekaru takwas na duhu yayin da aka kashe fitulun.

“Mayar da fitilun kan titi na cikin ƙoƙarin da sabuwar gwamnati ke yi na magance matsalar fashi da makami da sace-sacen waya da sauran miyagun ayyuka, musamman a babban birnin Kano.”

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya naɗa Akanta-Janar da shugabannin hukumomi huɗu

Aikin da ake ci gaba da gudanarwa ya fara tun ranar Talata kuma zai ci gaba har sai an kuɓutar da kowane ɓangare na jihar daga duhun da ke ba da mafaka ga masu aikata laifuka da ‘yan bangar siyasa,” in ji shi.


Comments

One response to “Gwamnatin Kano ta kafa kotunan tafi da gidanka domin magance satar waya”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta kafa kotunan tafi da gidanka domin magance satar waya […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *