Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da Sabon tsarin biyan haraji na zamani a Jihar

0
107
Gwamnatin Kano ta kaddamar da Sabon tsarin biyan haraji na zamani a Jihar

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da Sabon tsarin biyan haraji na zamani a Jihar

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kano (KIRS) ta ƙaddamar da sabon tsarin biyan haraji na zamani, wanda zai taimaka wajen sauƙaƙa biyan haraji tare da tabbatar da gaskiya da inganci a tsarin tattalin arzikin jihar.

Babban Daraktan Sashen Tabbatar da Biyan Haraji na hukumar, Muhammad Abba Aliyu, ya bayyana cewa sabon tsarin zai haɗa bayanan masu biyan haraji da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) domin gano masu kaucewa biyan haraji da kuma hana maimaita rajista.

Ya ce, tsarin zai bai wa jama’a damar biyan haraji ta hanyoyi daban-daban kamar ta yanar gizo, POS, ko kai tsaye ta banki, inda kudaden za su shiga asusun gwamnati kai tsaye ba tare da shiga hannun wasu jami’an hukumar ba.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta fara karɓar haraji daga hannun mata masu zaman kansu

Abba Aliyu ya roƙi al’umma da su ba da haɗin kai wajen biyan haraji domin tallafawa ayyukan ci gaban jihar, yana mai cewa wannan sabon tsarin zai kawo sauyi wajen karɓar haraji cikin gaskiya da sauƙi.

Leave a Reply