No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin Kano ta haramta muƙabala tsakanin Sha’irai mawaƙa, ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tazul Izzi

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta dukkan muƙabalar mawakan addini a jihar, sai dai idan an samu sahalewar hukumar tun kafin gudanar da su.

Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin kaddamar da kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Malam Isha Abdullahi, Daraktan Harkokin Musamman na hukumar.

El-Mustapha ya ce an ɗauki wannan mataki ne sakamakon muƙabalar da aka gudanar ba tare da izini ba tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi, wadda ya bayyana a matsayin karya ƙa’idodin hukumar.

KU KUMA KARANTA: Islamiyoyi sama da 700 ne suka halarci zagayen Maulidin Annabi Muhammad (SAWW) a Potiskum

Hukumar ta bai wa mawakan biyu tare da masu gabatar da muƙabalar wa’adin awanni 24 su bayyana gaban kwamitin binciken.

A cewar hukumar, shirya irin wannan muƙabala ba tare da amincewar ta ba ya sabawa dokar Tace Fina-finan Jihar Kano, kuma hakan na iya haifar da ɗaukar matakan shari’a masu tsanani.

Shugaban hukumar ya jaddada kudirin hukumar na ci gaba da tsarawa da kuma sa ido kan harkokin mawakan addini da masu nishadantarwa a jihar, bisa tanadin doka.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da tallafa wa hukumar da bayanai masu amfani da za su kawo zaman lafiya, fahimtar juna, da bunƙasar al’adu a jihar.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...