Gwamnatin Kano ta haramta amfani da Injinan sare bishiyoyi a faɗin jihar

0
241
Gwamnatin Kano ta haramta amfani da Injinan sare bishiyoyi a faɗin jihar

Gwamnatin Kano ta haramta amfani da Injinan sare bishiyoyi a faɗin jihar

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnatin Kano ta haramta amfani da zarton sare bishiyoyi ba da izini ba tare da cin tarar Naira dubu 500 ga waɗanda suka sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta amfani da injin sare bishiyoyi (chainsaw) ba tare da lasisi ba, inda masu karya doka za su fuskanci tara har naira dubu dari biyar (₦500,000), kwace kayan aiki da kuma yuwuwar zuwa gidan yari.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya bayyana cewa duk wanda ya sare bishiya ba tare da izini ba zai biya tara ta naira dubu dari biyu da hamsin (₦250,000) kan kowace bishiya, tare da umarnin dasa sabbin bishiyoyi.

Ya bayyana Hakan ne yayin taron manema labarai a ranar Talata a Kano.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta hana kafawa da manna mujallun tallace-tallace a jikin fitilun kan titi

Ya ce an samar da tsarin lasisin amfani da injin sare bishiyoyi da kuma izinin sare ko datse bishiya, domin samar da tsari da kuma dakile sare dazuka ba bisa ka’ida ba.

Hashim ya bayyana cewa tilasta bin dokar za a yi shi tare da jami’an tsaro, hukumomin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da masu sa ido na al’umma, tare da amfani da rajistar Internet don masu lasisi.

Ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnati na rage sare dazuka, dawo da dazukan da aka lalata, da kuma kare muhalli da albarkatun halitta na jihar.

Leave a Reply