Gwamnatin Kano ta hana kafawa da manna mujallun tallace-tallace a jikin fitilun kan titi

0
111
Gwamnatin Kano ta hana kafawa da manna mujallun tallace-tallace a jikin fitilun kan titi

Gwamnatin Kano ta hana kafawa da manna mujallun tallace-tallace a jikin fitilun kan titi

Hukumar Tallace-Tallace da Kafa Alamu ta Jihar Kano (KASA) ta bayar da umarnin a gaggauta cire dukkan tallace-tallacen kasuwanci da aka dora a sandunan fitilu a fadin jihar.

A cikin sanarwar da ta fitar, KASA ta bayyana cewa ba ta bayar da wani lasisi ko izini na amfani da fitilun kanta titi wajen manna mujallun tallace-tallace ba.

Ta gargadi masu amfani da su cewa hakan sabawa dokoki da ka’idojin hukumar ne.

KU KUMA KARANTA: Su waye suka sace fitilun titin tashan jirgin sama na Legas?

“Dole ne a gaggauta cire dukkan tallace-tallacen da aka dora a kan sandunan fitilu a cikin Jihar Kano ta hannun masu mallakarsu, domin kauce wa matakan doka daga hukumar,” in ji sanarwar.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa tana duba yiwuwar samar da tsarin doka na musamman da zai bai wa ‘yan kasuwa damar amfani da sandunan fitilu wajen tallata kayayyaki a nan gaba. Ta kuma tabbatar cewa za a sanar da masu ruwa da tsaki da zarar an amince da tsarin.

Leave a Reply