Gwamnatin Kano ta fara tantance ma’aikatan shara don biyan su haƙƙoƙinsu

0
22
Gwamnatin Kano ta fara tantance ma'aikatan shara don biyan su haƙƙoƙinsu

Gwamnatin Kano ta fara tantance ma’aikatan shara don biyan su haƙƙoƙinsu

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Ma’aikatar kula da Muhalli ta Jihar Kano ta fara tantance ma’aikatan shara, da ake wa laƙabi da (Sanitation Vanguard) su 2,369 domin biyan su haƙƙoƙinsu.

A kwanan ne gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da fitar da kudade don biyan ma’aikatan bashin albashin su na watanni 9.

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce Kwamishinan Ma’aikatar kula da Muhalli, Dakta Dahir M. Hashim ya bada umarnin tantance rukunin farko na ma’aikatan 1,000.

KU KUMA KARANTA:Gwamna Yobe ya amince da ƙarin wa’adin watanni 2 da a miƙa rahoton tantance ma’aikatan jihar

Sanarwar ta ce duk waɗanda abun ya shafa su tuntubi jami’o’in su na ƙananan hukumomi domin karɓar bayanai akan ranar da za a tantance su.

“Kamar yadda maigirma Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yananyi na Jihar Kano Dr. Dahir M Hashim yayi umarni, an cigaba da tantance dakarun tsafta na Jihar Kano (Sanitation Vanguard) su dubu ɗaya (1000) domin biya su haƙƙoƙinsu.

“Dan haka ana kira ga waɗanan ma’aikata da su tuntuɓi shugabanninsu karamar hukuma domin sani ranar da za’a tantancesu,” in ji sanarwar

Leave a Reply