Gwamnatin Kano ta biya haƙƙoƙin masu sharar tituna 2,000 albashinsu na watanni 8

0
14
Gwamnatin Kano ta biya haƙƙoƙin masu sharar tituna 2,000 albashinsu na watanni 8

Gwamnatin Kano ta biya haƙƙoƙin masu sharar tituna 2,000 albashinsu na watanni 8

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnatin ta Kano ta ce ta tantance ma’aikatan sharar su 2,369 da ta gada daga gwamnatin da ta gabata.

Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi Dr. Dahiru Muhammad Hashim wanda ya wakilci gwamna Abba a wajen taron kaddamar da biyan kudaden a ranar Laraba, ya raba wa ma’aikatan katin cirar kudi na ATM, wanda ya kawo karshen tsarin biyan kudi a hannu.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano ta fara tantance ma’aikatan shara don biyan su haƙƙoƙinsu

Dr Hashim ya ce hanyar biyan kudin ta hannu da ake amfani da ita a baya ta bada damar cin hanci da rashawa, yana mai jaddada cewa bullo da biyan kudin ta hanyar banki zai tabbatar da gaskiya da inganci.

Kwamishinan ya kuma bayyana shirin samar da sabbin kayan sawa (Uniform) da kayan kariya ga masu shara a tituna.

Haka kuma ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar Kano za ta bullo da shirin wanke wasu manyan tituna domin inganta tsafta a fadin Kano.

Leave a Reply