No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayar da umarnin rufe duk wani gidan gala da ake da shi a jihar.

Shugaban hukumar Abba El Mustapha ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

“A shirye-shiryen ta na shigowar watan Azumin Ramadana, Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta bayar da umarnin kulle dukkannin gidajen Galar da ke faɗin jihar Kano,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe gomman Falasɗinawa a ranar farko ta Azumin Ramadana

Hukumar ta ce ba ta ɗauki wannan mataki ba sai da ta zauna ta tattauna da jagororin musu gidajen galar da ke jihar.

Hukumar ta ce dokar za ta fara aiki ne tun daga jiya Lahadi har zuwa 1 ga watan Shawwal wato ranar bikin Ƙaramar Sallah.

A sanarwar, Abba El-mustapha ya gargadi masu gidajen wasannin na gala da su guji karya doka inda ya ce duk wanda hukumar ta samu da laifin karya wannan dokar to hakika za ta ɗauki mataki mai tsauri a kansa wanda ka iya sawa ya rasa lasisin sa na din-din-din.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...