Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kashe Boderi Isyaku ƙasurgumin dan-fashin dajin nan da ya addabi jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara Neja da Abuja, tare da wasu manyan ‘yan-bindigan da ke tare da shi.
Gwamnatin jahar Kaduna ta tabbatar da cewa Boderi Isyaku ne da ya jagoranci manyan hare-hare a jihar Kaduna da ma wasu maƙwabtan jahohi, inji muƙaddashin kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, malam Samuel Aruwan.
Masana harkokin tsaro irin su manjo Yahaya shinko mai-ritaya na ganin dole a jinjinawa jami’an tsaro kan wannan ƙoƙari amma ya ce wajibi su ci gaba ta tashi tsaye.
KU KUMA KARANTA:Za’a buɗe sabuwar ma’aikatar wutar lantarki a jihar Abiya
A hirar shi da Muryar Amurka, Alh. Ɗayyabu Kerawa wanda ya jagoranci al’ummar garuruwan da ke yammacin Zariya da su ka yi koke a kan yadda ‘yan-bindiga ke kai hare-hare a yankunan su, kuma ya ce jin labarin kashe ƙasurgumin ɗan-fashin dajin ya sa sun fara ji akwai yuwuwar su koma noma bana.
Cikin watan Fabarairun nan dai ‘yan-bindiga sun kai hare-hare a wasu yankunan ƙananan hukumomin Igabi, Giwa, Chukun, Ƙaura da Kajuru sai dai ana sa ran wannan nasarar kashe ‘yan-fashin dajin, ka iya kawo ƙarshen barazanar tsaro a waɗannan yankuna.