Gwamnatin Kaduna ta nisanta kanta akan bidiyon dukan Ɗan-Balki kwamanda

0
74
Gwamnatin Kaduna ta nisanta kanta akan bidiyon dukan Ɗan-Balki kwamanda

Gwamnatin Kaduna ta nisanta kanta akan bidiyon dukan Ɗan-Balki kwamanda

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umarnin gudanar cikakken bincike akan bidiyon da aka nuna ana dukan ɗan siyasar nan na Kano, Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda, wanda yake yawo a kafafen sada zumunta.

A cikin wata sanawar da aka raba wa manema  labarai a Kaduna ɗai ɗauke da sa hannun babban Sakataren yaɗa labarai na gwamnatin jihar Kaduna Muhammad Lawal Shehu, ya ce  gwamnatin ta nisanta kanta aka lamarin

“An ja hankalin gwamnatin jihar Kaduna game da wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda aka nuna wasu da ba a san ko su wa ye ba su na yi wa Ɗan Bilki Kwamandan bulala bisa zargin shi da zagin gwamna Uba Sani”

Sanarwar ta ci gaba da cewa “Gwamnatin jihar Kaduna dai ta nisanta kan ta daga wannan mummunan lamarin, ta na mai cewa hakan ba ya da hurumi a duk wata al’umma tagari, don haka ta na nan a kan bakar ta na mutunta tsarin bin doka da oda”

KU KUMA KARANTA: Su wa suka yi wa Ɗan-Bilki Kwamanda duka?

Haka kuma, gwamnatin jihar ta bayyana cewa tsarin shugabancin ta an gina shi ne a kan adalci da daidaito da kuma mutunta ɗan Adam.

Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta na maraba da shawarwarin al’umma, sannann ta buɗe ƙofar ta yadda kowa zai iya bayyana ra’ayin sa a siyasance.

Ta ce Gwamnan jihar Kaduna ya kwashe tsawon lokaci ya na fafutukar kare ‘yancin ɗan Adam, don haka har yanzu ya na kan bakar sa ta tabbatar da ganin ba a tauye haƙƙin kowane bil-Adama ba bisa tsarin doka da oda.

Tuni dai Gwamna Uba Sani ya bada umurnin a gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike a kan wannan mumman lamarin, sannan ya lashi takobin bin diddigin yadda lamarin ya faru, tare da bada tabbacin cewa duk mai hannu a aika-aikar dole ya fuskanci hukuncin abin da ya aikata.

Leave a Reply