Gwamnatin jihar Yobe ta fara aikin tituna da magudanan ruwa

3
248

Gwamnatin jihar Yobe ta hannun ma’aikatar ayyuka ta jihar, ta fara aikin gina tituna da magudanan ruwa a manyan garuruwa biyar na jihar.

Kwamishinan ma’aikatar ayyuka na jihar, Injiniya Umaru wakil, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin da yake zantawa da manema labarai a Damaturu.

Kwamishinan ayyukan ya yi nuni da cewa Gwamna Mai Mala Buni, ya jajirce wajen ganin ya kammala dukkan ayyukan da magabacin sa ya ƙaddamar tare da ci gaba da ƙaddamar da wasu sabbin hanyoyi, gadoji da magudanan ruwa a faɗin jihar baki daya.

Injiniya Wakil ya bayyana cewa manyan garuruwan biyar da za su ci gajiyar ayyukan ci gaban ababen more rayuwa sun haɗa da Damaturu, da ke da titin gari na kusan kilomita 10 da magudanar ruwa da za a yi. Sai Potiskum na da tituna da magudanan ruwa 4.2, sai Nguru na da titin kilomita 3.3, da magudanan ruwa, Gashua mai tsawon kilomita 3.2, tituna da magudanan ruwa da Geidam mai nisan kilomita 4.6 da magudanan ruwa.

KU KUMA KARANTA: Yadda Buhari ya ƙaddamar da ayyukan Gwamna Buni na jihar Yobe

Ya ce, Gwamna Buni na cike da burin samar da ababen more rayuwa a jihar duk da haɗakar albarkatun da yake da ita ba zai rasa nasaba da kishinsa na inganta rayuwar ‘yan ƙasa ta fuskar zamantakewa da tattalin arziƙi ba.

Injiniya Umaru Wakil ya ci gaba da cewa, an shirya yadda za a gina titin kilomita 22.5 daga Fika zuwa Maluri mai tsawon kilomita 1,18 daga Bukarti zuwa Toshia, da sake gina titin kilomita 18 daga Jaji-maji zuwa Karasuwa mai nisan kilomita 4 daga babbar hanyar Nguru, ta karaso zuwa Galu.

Injiniya Wakil ya bayyana cewa sauran ayyukan da za a aiwatar sun haɗa da gina titin Kukuri-Dawasa kilomita 16, Fadawa-Daya kilomita 25, titin Damaturu-kalallawa-Gabai mai nisan kilomita 18, titin Damchuwa-Garin Bingel da dai sauransu.

3 COMMENTS

Leave a Reply