Gwamnatin jihar Kano za ta biya wa ɗalibai 55,000 kuɗin rubuta jarabawar NECO

Ɗaya daga cikin manufofin gwamnatin jihar Kano na mayar da ɓangaren ilimi matsayi da kuma ba shi kulawar da ake buƙata, gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan kuɗin NECO ga ɗaliban makarantun gwamnati su dubu hamsin da biyar (55,000) nan take domin samun damar rubuta jarabawar SSCE (NECO) a shekarar 2023.

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar lahadi, ya ce gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin kwanaki ashirin da suka gabata a gidan gwamnati.

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci ɗaliban da suka amfana da su yi aiki tuƙuru don ganin an samu sakamako mai kyau sannan kuma su mayar da hankali wajen ganin sun tabbatar da ɗimbin jarin da gwamnatin jihar ta yi don gudun ka da su daina neman ilimi.

KU KUMA KARANTA: JAMB ta biya biliyan 1.5 ga cibiyoyin shirya jarabawa ta CBT

A cewar Gwamnan, “A matsayina na gwamnatin da abin ya shafa, mu tabbatar da cewa ba a daina ci gaban karatun ku na neman ilimi ba, kuma nan take na amince da biyan kuɗin jarabawar ga ɗalibai dubu 55,000 a faɗin jihar nan.

Ya kamata ku yi iya ƙoƙarinku kuma ku jajirce domin ku fito da kyakkyawan sakamakon jarrabawar da za ku iya farantawa jihar da iyalanku da kuma alfahari da ku” Gwamnan ya yi gargaɗi.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa na fito da manufofi da tsare-tsare na inganta harkar ilimi, domin ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma.


Comments

One response to “Gwamnatin jihar Kano za ta biya wa ɗalibai 55,000 kuɗin rubuta jarabawar NECO”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Gwamnatin jihar Kano za ta biya wa ɗalibai 55,000 kuɗin rubuta jarabawar NECO […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *