Gwamnatin Jigawa ta bankaɗo ma’aikatan bogi 6,348
Gwamnatin Jigawa ta bayyana cewa ta bankado ma’aikatan bogi 6,348 yayin aikin tantance ma’aikatanta ɗaya gudana a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Sagir Musa ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar yau Talata a birnin Dutse.
Ya ƙara da cewar rahoton aikin daukar bayanai da tantance ma’aikatan da aka gudanar a fadin jihar, ya nuna cewa an gano ma’aikatan bogi 6, 348 tare da alkintawa jihar Naira miliyan 314 a kowane wata.
KU KUMA KARANTA: Ƙasar Nijar ta bankaɗo makatan bogi sama da dubu 3 da ake biya albashi
A cewar Sagir Musa, majalisar zartarwar jihar ta yi nazarin rahoton tare da kafa cibiyar cigaba da daukar bayanan ma’aikata a ofishin shugaban ma’aikatan jihar.
Ya ce, hakan zai hanzarta kammala aikin daukar bayanai da tantance ma’aikatan da ake yi.