Gwamnatin Ghana ta rage kuɗin wutar lantarki

Hukumar da ke sa ido kan biyan biyan kuɗaɗen wuta da ruwa da sauran kayan amfani a ƙasar Ghana ta rage kuɗin wutar da za a biya a ƙasar da kashi 1.52 cikin 100.

Sai dai ƙarin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta PURC ta yi ƙarin kuɗin da za a rinka biya na ruwa a ƙasar da kashi 0.34 a cikin 100 a rubu’i na karshe na shekarar 2023.

Kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito cewa wannan sabon gyaran da aka yi a farashin wuta da ruwa zai soma aiki ne daga 1 ga watan Disambar 2023 zuwa 29 ga watan Fabrairun 2024.

KU KUMA KARANTA: Ma’aikatan wutar lantarki sun garƙame hedikwatar KEDCO ta jihar Kano

Sakamakon wannan ƙarin da aka yi, masu zama a unguwannin marasa galiho za su soma biyan Cedi 0.6348 a duk kWh idan aka kwatanta da 0.6446 da suke biya a halin yanzu.

Sai kuma sauran jama’a za su rinka biyan Cedi 1.40 a duk kWh daga Cedi 1.42 da suke biya a baya.

Ga kuma masu amfani da ruwa a cikin gidaje, za su soma biyan Cedi 4.7401 a duk m3 daga 1 ga watan Disamba a maimakon 4.7239 da suke biya a halin yanzu.

Sai kuma wuraren da ba gidaje ba za su rinka biyan Cedi 14.19 a duk m3 a maimakon 14.1394 da uske biya, sai kuma wuraren kasuwanci za su rinka biyan Cedi 25.38 daga 25.2962 da suke biya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *