Gwamnatin Filato ta dakatar da haƙar ma’adinai saboda matsalar tsaro

0
7
Gwamnatin Filato ta dakatar da haƙar ma’adinai saboda matsalar tsaro

Gwamnatin Filato ta dakatar da haƙar ma’adinai saboda matsalar tsaro

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayar da umarnin dakatar haƙar ma’adanai a faɗin jihar daga ranar 21 ga watan Fabrairu, 2025.

Ya yanke wannan shawara ne saboda ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida wanda ke da alaƙa da laifuka da suka shafi ta’addanci, satar mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma, ya ce yawan baƙi da ke shiga yankunan da ake haƙar ma’adanai na ƙara haddasa matsalar tsaro.

Akwai ƙaruwar ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, wanda ke haifar da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na jihar.

“Haka kuma, yawan baƙin da ke shiga yankunan haƙar ma’adanai na ƙara yawan laifuka kamar ta’addanci, garkuwa da mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi,” in ji Gwamna Mutfwang.

Domin shawo kan wannan matsala, gwamnatin ta kafa kwamitin da zai binciki waɗanda ke da izinin haƙar ma’adanai da kuma ƙirƙirar tsarin kula da ayyukan haƙar.

KU KUMA KARANTA:Ana zargin sabuwar ƙungiyar ACHAD da safarar mutane a jihar Filato

Gwamnan ya ƙara da cewa za su yi aiki tare da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da tsare-tsaren doka da kuma inganta matakan tsaro.

“Za mu haɗa kai da Gwamnatin Tarayya domin bitar yadda ake sanya ido kan ayyukan haƙar ma’adanai.

“Haka kuma, za mu tabbatar da cewa kamfanonin haƙar suna bai wa al’umma gudunmawa,” in ji shi.

Gwamnan ya yi alƙawarin duba matsalar tsaro a yankunan da ake haƙar ma’adanai gaba ɗaya tare da tabbatar da cewa kamfanonin haƙar ma’adanai suna taimaka wa al’ummomin yankunan da suke aiki a cikinsu.

Leave a Reply