Gwamnatin Edo ta ƙara albashi mafi ƙaranci zuwa dubu 40,000, ta rage ranakun aiki zuwa sau uku a mako

0
674

Gwamnatin jihar Edo ta sanar da cewa ta ƙara albashi mafi ƙaranci daga N30,000 zuwa naira dubu 40,000 duk wata domin rage raɗaɗin tattalin arziƙin da ake samu sakamakon cire tallafin man fetur.

Har ila yau, gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta rage yawan kwanakin zuwa aiki daga sau biyar zuwa sau uku a cikin mako guda ga ma’aikatan jihar.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar laraba, 7 ga watan Yuni.

Gwamnan jihar ta baiwa ma’aikata tabbacin cewa jihar za ta tallafa musu ta kowace hanya domin rage raɗaɗin tattalin arziƙi da cire tallafin da ake samu.

KU KUMA KARANTA: Ya kamata a duba batun ‘mafi ƙarancin albashi’, Tinubu ya gayawa gwamnonin APC

“Bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, farashin man fetur ya ƙaru a ƙasar wanda ya kai ga tashin farashin kayayyaki da ayyuka da kuma tsadar rayuwa baki ɗaya,” in ji ta.

“A matsayinmu na gwamnati mai fafutuka, tun daga nan muka ɗauki matakin ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata a jihar Edo daga dubu 30,000 da aka amince da shi zuwa dubu 40,000, wanda shi ne mafi girma a ƙasar a yau.

“Muna so mu tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da biyan wannan kuɗi, yayin da muke fatan ƙara yawan kuɗaɗen da za a samu idan aka samu ƙarin kaso daga gwamnatin tarayya a jihar mu bisa la’akari da tanadin da ake sa ran za a samu ta hanyar cire tallafin man fetur.

“Mun san wahalhalun da wannan manufa ta haifar wanda ya ƙara tsadar sufuri, tare da cin buri a cikin albashin ma’aikata a jihar.

“Saboda haka, gwamnatin jihar Edo za ta rage yawan kwanakin aiki da ma’aikatan gwamnati da na gwamnati za su riƙa zuwa wuraren ayyukansu daga kwana biyar a mako zuwa kwana uku a mako har sai an sanar da su.

Ma’aikata yanzu za su yi aiki daga gida kwana biyu a kowane mako, “in ji sanarwar.

Obaseki ya ƙara da cewa, jihar na kuma ƙoƙarin samar da ƙarin azuzuwan karatu, ta yadda za a rage tsadar zirga-zirgar iyaye da malamai da ɗalibai zuwa makaranta.

“Hukumar Edo SUBEB za ta bayar da cikakkun bayanai kan wannan shiri a cikin kwanaki masu zuwa.

Domin rage tsadar wutar lantarki ga jama’armu, za mu ci gaba da haɗa kai da kamfanonin wutar lantarki a jihar domin inganta samar da wutar lantarki ga gidaje da kasuwanci.

“Hakazalika, ana samar da hanyoyin haɗin ‘fiber optic’ don taimakawa mutanenmu suyi aiki daga nesa, ta yadda za su rage farashin sufuri.”

A baya jaridar Neptune Prime ta bayar da rahoton cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da dakatar da tallafin man fetur bayan da gwamnatin da ta shuɗe kawai ta yi tanadin tallafin har zuwa ƙarshen watan Yuni.

Sanarwar ta haifar da tashin gwauron zabin farashin man fetur daga manyan ‘yan kasuwar man da suka haɗa da Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) Limited.

Leave a Reply