Gwamnatin Binuwai za ta rufe makarantu 2,100 a faɗin jihar

0
41
Gwamnatin Binuwai za ta rufe makarantu 2,100 a faɗin jihar

Gwamnatin Binuwai za ta rufe makarantu 2,100 a faɗin jihar

Hukumar tabbatar da ingancin ilimi ta jihar Binuwai (BEQA) ta gano makarantun firamare da sakandire 2,100 da za a rufe a matakin farko na shirin yaƙi da gurbatattun makarantu a jihar.

Dr. Terna Francis, Darakta Janar na BEQA ne ya bayyana hakan a ranar Laraba lokacin da ya halarci bikin bayar da kyaututtuka ga ɗalibai masu hazaƙa a makarantar Templegate Academy da ke Makurdi a matsayin babban bako na musamman.

KU KUMA KARANTA:Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 2 a Benuwai

Yayin da ya ke miƙa kyautar ga wasu zaɓaɓɓun ɗalibai ‘yan aji 6 zuwa 7, Francis ya ce ya kamata mamallaka makarantu su daina matsa wa iyaye da sunan kammala karatun ‘ya’yan su kasancewar an daina bada satifiket.

Francis ya bayyana cewa an gano makarantu 2,100 da za a rufe a matakin farko na dakatar da makarantun da ba su da aminci, inda ya kara da cewa makarantun da suka karbi fom ɗin tantancewa da kuma kammala matakan da suka dace ya kamata su zo domin karɓar takardar shaidar amincewarsu, wanda a yanzu ya zama amincewar hukuma.

Ya kuma yabawa iyaye bisa jajircewar da suka yi na samar da ingantaccen ilimi ga ‘ya’yansu, sannan ya yabawa makarantar bisa ƙoƙarin da take yi, inda ya bayyana cewa a ziyarar da yake yi ba tare da ɓata lokaci ba, ya lura cewa gaba ɗaya bayanan karatu na makarantar na da gamsarwa.