Gwamnatin Bauchi ta bai wa ɗalibai 4 da suka yi bajinta a JAMB kyautar ₦4m

0
26
Gwamnatin Bauchi ta ya bai wa ɗalibai 4 da suka yi bajinta a JAMB kyautar ₦4m

Gwamnatin Bauchi ta bai wa ɗalibai 4 da suka yi bajinta a JAMB kyautar ₦4m

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bai wa ɗalibai huɗu ’yan asalin jihar da suka fi cin jarabawar JAMB ta 2024 kyautar kuɗi Naira miliyan huɗu.

Ɗaliban sun haɗa da Kawthar Shehu wadda ta samu maki 348, Geoffrey Yakubu mai maki 347.

Sauran sun haɗa da Abdullahi Garba wanda ya samu maki 347, da kuma Magaji Umar mai maki 333.

Da yake magana lokacin gabatar da kyautar a ranar Talata, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Bauchi, Yahuza Adamu, wanda ya wakilci gwamnan.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura

Ya ce an bayar da kyautar ne don ƙarfafa wa ɗaliban gwiwa domin su dage wajen samun nasara a karatunsu.

Leave a Reply