Gwamnatin Bauchi ta kori babban ma’aikacin gwamnati bisa zargin badaƙalar miliyan uku

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin Bauchi ta kori babban ma’aikacin gwamnati bisa zargin badaƙalar albashin Naira miliyan uku. Hukumar ma’aikata ta jihar Bauchi (BSCSC), ta kori Ibrahim Garba, babban mataimakin sakatariyar hukumar fansho ta jihar bisa zargin “mummunan damfara na albashi da fansho”.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na BSCSC, Saleh Umar, ya fitar a Bauchi ranar Talata. Hukumar ta yi zargin cewa matakin na Mista Garba ya saɓa wa dokar ma’aikatan gwamnati, PSR, 0327(XI) da ta shafi almubazzaranci.

Hukumar ta amince da dakatar da zaman ne a zamanta na 17 da aka yi a ranar 1 ga watan Agusta, “Kwamitin ladabtarwa na hukumar fansho ta jihar ta samu Garba da laifin musanya asusun ajiyar wani Audu Mohammed, wanda yanzu ya rasu da nasa.

KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yan sandan Legas ta kori jami’in da ya saci jaririya

“Hakan ya taimaka wajen sauya wurin biyan albashi bayan ‘yan uwan ​​mamacin sun kai rahoton rasuwarsa. “Bayan haka, ya karɓi fansho ba bisa ƙa’ida ba na tsawon watanni 55 Naira 54,871 na tsawon shekaru huɗu da watanni bakwai wanda ya kai sama da Naira miliyan uku.

“Za a ƙwato wannan adadin daga wurin Garba,” in ji shi. Ya kuma bayyana cewa shugaban hukumar Abubakar Usman ya yi ƙira ga ma’aikata a jihar da su ji tsoron Allah wajen gudanar da ayyukansu.

Ya ce dole ne a kiyaye PSR kuma a bi shi a matsayin jagora Shugaban hukumar ya tabbatar wa da ma’aikatan jihar cewa babu wani ma’aikaci da za a ci zarafinsa ba don komai ba kuma hukumar ba za ta naɗe hannunta ba yayin da miyagu ke yi wa jiha zagon ƙasa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *