No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin Amurka ta bai wa Najeriya tallafin abinci na dala miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5 ga Shirin Abinci na Duniya (WFP) domin samar da tallafin abinci da na abinci mai gina jiki ga ‘yan Najeriya, musamman ma waɗanda rikice-rikice suka raba da muhallansu.

Wannan tallafi zai bai wa WFP damar kai agajin abinci da kula da lafiyar gina jiki ga mutum 764,205 a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Najeriya da rikici ya shafa.

KU KUMA KARANTA: UNICEF ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su shiga ayyukan jin ƙai, sakamakon janye tallafin Gwamnatin Amurka

A cewar shirin, daga cikin masu amfana akwai mata masu juna biyu da masu shayarwa 41,569, da kuma yara 43,235, waɗanda za su karɓi tallafin abincin.

Shirin ya ce wannan taimako daga gwamnatin Amurka na da matuƙar muhimmanci wajen ceto rayuka da rage matsalar yunwa da rashin abinci mai gina jiki a yankunan da rikici ya daɗe yana addaba.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...