Gwamnati ta sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya balaguro saboda Kirismeti

0
139

A wani mataki na rage wahalhalun da ake fama da shi na tafiye-tafiyen hutu, gwamnatin Najeriya ta ɓullo da wasu matakai na kai ɗauki ga ‘yan ƙasar a lokacin bukukuwa.

Sanarwar, wacce gwamnatin ƙasar ta fitar, ta ce shirin ya haɗa da zirga-zirgar jiragen ƙasa kyauta da kuma rage kashi 50% na farashin motocin bas a faɗin ƙasar.

Dele Alake, shi ne ministan ma’adanan kuma shugaban kwamitin ma’aikatun ƙasa da ƙasa kan tsoma baƙin shugaban ƙasa, ya jaddada cewa shirin na da nufin baiwa matafiya a cikin gida damar ziyartar ‘yan uwansu da garuruwan su ba tare da damuwa da karin nauyi da tsadar kuɗin sufuri ba.

An yankewa matafiya a cikin jihohin ƙasar kuɗin shiga jirgin ƙasa, wanda aka tsara zai fara aiki daga ranar 21 ga Disamba zuwa 4 ga Janairu, abin da ya kasance wani shirin haɗin gwiwa ne tare da kamfanonin da ke aiki da manyan motoci a kan hanyoyi 22 a faɗin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Ghana ta rage kuɗin wutar lantarki

Ministan ya ƙara da cewa, shugaba Bola Tinubu ya amince da wannan shiri, wanda musamman ya fi mayar da hankali ga talakawa, da ke fafutukar yadda za su ciyar da iyalansu.

Ministan Sufuri Sa’idu Alkali ya bayyana aniyar gwamnati na ganin cewa an samu raguwar farashin motocin bas da kuma samar zirga-zirgar matafiya a jirgin ƙasa kyauta domin sanya walwala a zukatar ‘yan ƙasar da kuma rage musu raɗaɗin tsadar sufuri.

Segun Falade, mai magana da yawun ƙungiyar ma’aikatan sufurin mota ta ƙasar, ya tabbatar da cewa masu motocin bas za su bi farashin kuɗin da da aka amince da su, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito.

Wannan ƙoƙari na haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki na harkokin sufuri na da nufin saukaka wa ‘yan ƙasa matsalar kuɗi a lokacin ake samun tangardar nauyin tafiye-tafiye a Najeriya, inda ake samu mafi yawan fasinjojin jiragen sama, da masu bin jiragen ƙasa a watan Disamba.

Leave a Reply