Gwamnati ta raba wa mata masu ƙaramin ƙarfi injin niƙa a jihar Edo

0
195

Ma’aikatar Ayyukan Gona da Samar da Abinci ta ƙasa ce ta raba kayan a wani mataki na wadata ƙasa da abinci.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) an ba kowacce daga cikin mata 15 ɗin kyautar injin niƙa guda ɗaya.

Babban Jami’i a ma’aikatar, Peter Pindar, ya ce an raba kayan ne ƙarƙashin shirin samar da tallafi ga mata da matasa kan hanyoyin sarrafa doya da adana ta domin ci gaban ƙasa.

A cewar Peter, ma’aikatar ta sayo injinan ne domin raba su ga mata a wani mataki na ƙarfafa musu gwiwa.

Leave a Reply