Gwamnan Zamfara ya karɓi baƙuncin ministan agaji, ya nemi ƙarin tallafi ga ‘yan gudun hijira a jihar

0
248

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Dauda Lawal, a ranar Alhamis, ya nemi ƙarin tallafi ga ‘yan gudun hijira a faɗin jihar Zamfara.

Gwamnan ya roƙi tallafin ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da fatara, Dakta Betta Edu a jihar Zamfara.

Sanarwar da kakakin Gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce, Ministar ta ziyarci jihar Zamfara ne domin buɗewa tare da miƙa gidaje 40 da aka kammala kuma na aiki a matsayin aikin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira.

Ya kuma ƙara da cewa Gwamnan ya raka Ministan Agaji domin ziyartar Jami’ar Tarayya ta Gusau, inda suka gana da hukumomin jami’ar da ɗaliban da aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun ƙuɓutar da ɗaliban jami’a shida waɗanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Zamfara

Sanarwar ta ƙara da cewa: “A jawabinsa a wurin buɗe taron, Gwamna Lawal ya yaba da ƙoƙarin sauran hukumomin tarayya kamar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA) kan irin tallafin jin ƙai da taimakon da suka yi wa jihar tsawon shekaru da dama. kwanan nan.

“Ya ce sanannen abu ne cewa jihar Zamfara na fuskantar ƙalubalen tsaro, kuma za a iya magance waɗannan matsalolin ne ta hanyar ingantaccen haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya, da jihohi maƙwabta, da duk masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro. Fiye da kome, dole ne mu riƙa yin abin da yake daidai a lokacin da ya dace.

“Lawal ya ƙara nanata cewa, abin takaici ne a yarda cewa ‘yan fashi suna talauta mata da yara, da mayarsu marayu da zawarawa da kuma ‘yan gudun hijira musamman a yankunan karkara. Wannan ya sanya jiha a sahun gaba a jerin manyan wuraren tashe-tashen hankula da marasa galihu a Jihohin Arewa maso Yamma da sauran al’ummar ƙasar baki ɗaya.

“Game da birnin na sake tsugunar da jama’a a jihar Zamfara, ya kamata a lura da cewa tun da aka kafa wannan gwamnati, muna magance matsalar ‘yan gudun hijira a duk sassan jihar. Samar da wurin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira a babban birnin jihar Gusau abin farin ciki ne.

“Mun yaba da ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi na rage raɗaɗin wahalhalun da al’ummarmu ke ciki.

Da take gabatar da nata jawabin, mai girma ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da fatara, Dakta Betta Edu, ta yabawa gwamna Dauda Lawal bisa namijin ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da jin daɗin ‘yan gudun hijira a faɗin jihar.

“Na yi matuƙar farin ciki da halartar wannan gagarumin buki na buɗewa tare da miƙawa gwamnati da al’ummar Jihar Zamfara garin sake tsugunar da jama’a a hukumance domin amfanin al’umma.

“Ina so in miƙa godiyata ga Gwamna Lawal, wanda ya tausaya wa halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki a Jihar.

“Na ji dukkan koke-koken da gwamnatin jihar ta yi, zan miƙa saƙon ga shugaban tarayyar Najeriya da ya ƙara tallafa wa ‘yan gudun hijira a Zamfara.

“Masu cin gajiyar waɗannan gidaje kuma za su ci gajiyar tallafin kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke yi duk wata domin rage tasirin cire tallafin man fetur,” inji ta.

Leave a Reply