Connect with us

Labarai

Gwamnan Zamfara ya jinjinawa jami’an tsaro tare da yin jaje ga wanda iftila’in ya shafa

Published

on

Gwamnan Zamfara ya jinjinawa jami’an tsaro tare da yin jaje ga wanda iftila’in ya shafa

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya jinjinawa ƙoƙarin jami’an tsaro na haɗin gwiwa game da sabbin hare-hare da nasarorin da suke samu a kan ‘yan bindiga a jihar.

A ƙarshen makon da ya gabata, rundunar sojojin ƙasar nan ta aika da wasu ƙarin jami’anta, a wani yunƙuri na sake fatattakar ayyukan ‘yan bindiga a yankunan da abin ya yi ƙamari a jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau, ya bayyana dirar mikiyar da sojojin suka yi wa ‘yan bindigar a matsayin mataki na dagula harkokin miyagun ‘yan ta’addan a Zamfara.

Sanarwar ta kuma jajanta wa al’ummomin da harin ‘yan bindigar ya shafa a ‘yan kwanakin nan, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana nan tana ci gaba da baiwa jami’an tsaro cikakken haɗin kai don shawo kan lamarin.

KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yansanda ta ba da naira miliyan 50 ga iyalan ‘yansanda da suka mutu a Zamfara

Sanarwar ta ce: “Ayyukan yaƙin da sojoji ke gudanarwa a wuraren da rashin tsaro ya yi ƙamari a Zamfara, abin a yaba ne, musamman bisa la’akari da irin nasarorin da aka samu tun lokacin fara ƙaddamar da munanan hare-hare kan ‘yan ta’addan a ƙarshen makon da ya gabata.

“Wannan aiki ya samu gagarumar nasara a yankunan ƙananan hukumomin Bunguɗu, Tsafe, Maru, da Zurmi, wanda ta kai ga hallaka wani ƙasurgumin ɗan’ta’adda, Abu Ɗan Dunkwuifa, wanda ya yi fice wajen addabar wasu ƙauyuka a Bunguɗu da Maru.

“A ƙauyen Magama Mai Rake ta yankin Ɗansadau da ke Ƙaramar Hukumar Maru, jami’an tsaron sun samu nasarar hallaka gomomin ‘yan ta’adda.

“Harin da sojoji suka sake kai wa a Nasarawan Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum ya yi sanadiyyar ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su a ƙauyukan Kamaru, Tungar Rogo, da Matsare, tare da ƙwato shanu da dama da aka sace.

“Jita-jitar cewa an yi garkuwa da mutane sama da 500 ba gaskiya ba ne ta wasu mutane da ba sa son zaman lafiya ya dawo Jihar Zamfara. Mafi akasarin yankunan da ke fama da rashin zaman lafiya a Zamfara na ci gaba da samun taimakon soji, inda ake samun sakamako mai kyau.

Gwamnan ya kuma jajanta wa al’ummar da ’yan bindiga suka kai wa hari a jihar.

“Gwamnatin jihar Zamfara na son nuna alhini ga al’ummomin da ’yan bindiga suka kai wa hari kwanan nan. Mun himmatu sosai wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Gwamnatinmu za ta ci gaba da tallafawa sojojin da ke yaƙi da rashin tsaro tare da bayar da duk wani tallafin gaggawa ga waɗanda rikicin ‘yan bindiga ya shafa a jihar.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like