Daga Ibraheem El-Tafseer
A ranar Litinin ne Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta jihar Zamfara.
A wajen taron, Gwamna Dauda Lawal ya karɓi bayani daga kwamitin da aka kafa domin tabbatar da matsayin kuɗaɗen fansho na jihar Zamfara da na ƙananan hukumomi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce taron da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnati da ke Gusau, an tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban jihar Zamfara.
Ya ƙara da cewa majalisar ta samu rahoton ci gaban da aka samu na sabunta biranen da ake yi a babban birnin jihar da kuma ƙarin bayani kan shirin ingantawa da zamanantar da filin wasa na tunawa da Sardaunan Gusau da dai sauransu.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwar Maru, bayan harin ‘yan bindiga a garin
Ya ce: “A ranar 9 ga Oktoba, 2023, Majalisar zartaswa ta Jihar Zamfara ta kafa wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikata, domin tantance matsayin da Jihar Zamfara ta ke da shi na bayar da gudunmawar fansho na ƙananan hukumomi.
“Yayin da yake yiwa majalisar bayani, Barista shugaban kwamitin kuma shugaban ma’aikata na jihar Zamfara Ahmad Aliyu Liman ya bayyana cewa manufar kwamitin ita ce ta binciki zargin karkatar da kuɗaɗen da aka zaftare daga albashin ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomin jihar kan shirinsu na fansho.
“Waɗannan kuɗaɗe ya kamata a miƙa su ga masu kula da asusun fansho (PFAs) waɗanda ke da alhakin kula da asusun ajiyar ma’aikata (RSAs) a jihar.
“Shugaban kwamatin ya bayyana cewa rashin fitar da kuɗaɗen ya saɓawa dokar fensho ta sake fasalin doka (2014) da ke tafiyar da tsarin tafiyar da kuɗaɗen fansho kamar yadda hukumar fansho ta ƙasa (PenCom) ta tsara.
“Ya kuma ƙara nanata cewa rashin kuɗin da aka samu ya haifar da gazawar Hukumar Kula da Kuɗaɗen Fansho (PFAs) ta ƙasa biyan kuɗin fansho da na mutuwa ga waɗanda suka dace, wanda hakan ya haifar da koma baya ga kuɗaɗen da ba a biya ba a halin yanzu ya yi wa Gwamnatin Jiha yawa.
“Gwamna Lawal a matsayinsa na Shugaban Majalisar Zartaswa, ya bayyana aniyar bayar da tallafin da ya dace don sasanta duk wani abu da ba a biya ba.