Gwamnan Yobe ya ƙaddamar da tallafin Naira biliyan 2.93 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

0
22
Gwamna Yobe ya ƙaddamar da tallafin Naira biliyan 2.93 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

Gwamnan Yobe ya ƙaddamar da tallafin Naira biliyan 2.93 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON, ya ƙaddamar da rabon tallafin Naira biliyan 2.93 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa, marasa galihu da masu ƙananan sana’o’i a jihar.

A wata takarda da Mamman Mohammed ya fitar, babban Daraktan yaɗa labarai na Gwamnan, ya ce Gwamna Buni a lokacin da yake ƙaddamar da rabon kuɗaɗen, ya ce shirye-shiryen tallafin da gwamnatin jihar Yobe ke yi na da nufin ƙarfafawa ‘yan ƙasa ne, da sake farfaɗo da fata, da kuma ƙarfafa ƙarfin da suke da shi domin tunkarar mummunan bala’in ambaliyar ruwa na 2024 ya haifar.

Gwamnatin jihar na tallafa wa mutane 25,500 da ambaliyar ruwa ta shafa da marasa galihu da Naira 50,000 kowannensu da kuma masu ƙananan ‘yan kasuwa 15,000 da Naira 100,000 kowanne.

Ya ce jihar Yobe ta samu rahoton ambaliyar ruwa da ba a taɓa yin irinsa ba a bana wanda ya raba al’umma 441 a faɗin ƙananan hukumomi 17 da ke faɗin jihar, lamarin da ya shafi gidaje sama da 20,000 tare da mutuwar mutane 34.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya amince da ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

A cewar Gwamna Buni, babbar hanyar Damaturu zuwa Bayamari ta lalace biyo bayan ambaliyar ruwa a wurare huɗu daban-daban a Kariyari, Jumbam, Koromari da Bayamari, yayin da titin tarayya ta Damaturu zuwa Buni Yadiya tafi tsakanin Katarko da garin Gujba.

“Haka zalika, ruwan ya yanke hanyar Potiskum zuwa Garin Alkali a Tarajim, sannan ya yanke hanyar Gaidam zuwa Bukarti a Mozagun.

“Gwamnatin jihar ta yi gaggawar aiwatar da duk hanyoyin da aka lalatar da su tare da katse al’ummomin da abin ya shafa zuwa sauran sassan jihar domin dawo da zirga-zirgar jama’a, kayayyaki da ayyuka.

“Gwamnatin jihar ta kuma yi irin wannan aikin a kan hanyar Gadaka zuwa Godowoli, Dogon kuka, hanyar Daura.

Ruwan, ya kuma lalata gine-ginen jama’a, gidajen mutane, gonaki da dabbobi da sauransu.

Gwamnan ya ce tun da farko gwamnatin jihar Yobe tare da goyon bayan gwamnatin tarayya da kuma ƙungiyoyin raya ƙasa sun raba kayan abinci da kuma kuɗaɗe miliyan 100 na agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa a ƙananan hukumomin da abin ya auku.

Ya kuma nanata ƙudurin gwamnatinsa na shirin ‘Renewed Hope Initiative’ na ba da tallafi ga mata, naƙasassu, tsofaffi, da sauran marasa galihu.

“Gwamnati za ta ci gaba da samar da ilimi kyauta, samar da kiwon lafiya mai rahusa, ci gaban fasaha da ƙarfafa tattalin arziƙi don ƙarfafa wa masu ƙaramin ƙarfi don bunƙasar tattalin arziƙi.” inji shi.

Leave a Reply