Gwamnan Yobe ya ziyarci ƙaramin ministan tsaro, don ci gaba da inganta harkar tsaro a jihar

0
338

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON, ya kai ziyara ta musamman a ofishin ƙaramin ministan tsaro Alhaji Bello Mattawale a Abuja.

Gwamna Buni ya gana da Ministan domin tattauna batutuwan haɗin gwiwa tsakanin jihar da ofishin domin ƙarfafa tsaro a jihar.

Ya ce duk da a halin da ake ciki yanzu tsaro ya inganta sosai a faɗin jihar amma, za a yi amfani da kowace dama wajen ɗaukar matakan kan-da-garki don magance matsalar tsaro a jihar.

“Akwai ci gaban tsaro da kwanciyar hankali a jihar Yobe. Amma duk da haka, ba za mu zauna mu saki ƙafa wajen ci gaba da jan ɗamara wajen daƙile yunƙurin ɓata gari ba.”

“Za mu ci gaba da tuntuɓar dukkan hukumomin tsaro domin tsara dabarun inganta zaman lafiya da tsaro a jihar Yobe.”

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya jagoranci taro don samar da tsaro mai inganci a jihar

“Na yi farin ciki kuma na gamsu da tabbacin da mai girma Minista ya bayar na inganta tsaro ga rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar.” in ji Gwamna Buni.

Ya kuma ba da tabbacin gwamnatin sa na goyon bayan hukumomin tsaro da ke aiki a jihar.

“Ina kuma ƙira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya ta hanyar ba su bayanai masu amfani a kan lokaci a duk lokacin da suka ga wasu take-taken da ba su lamunta ba.” Gwamnan ya jaddada

A nashi ɓangaren, Ministan ya bai wa Gwamna Buni tabbacin cewa gwamnatin tarayya wajen amfani da duk wata damar da ta dace don kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Ya yaba wa Gwamna Buni bisa jajircewar sa da bin dukkan hanyoyin da suka dace wajen tabbatar da tsaro ya inganta harkokin tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Leave a Reply