Daga Ibraheem El-Tafseer
Mai Girma Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni CON (Chiroman Gujba) a ranar Asabar 2 ga Satumba 2023, ya karɓi baƙuncin babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar TA Lagbaja wanda ya kai wa Gwamnan ziyara a gidan gwamnati da ke birnin Damaturu.
Da yake maraba da babban hafsan hafsoshin sojan ƙasan, Gwamna Buni ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da neman goyon baya da haɗin kan sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro a kowane lokaci.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Yobe ta raba kayan abinci a Potiskum, don rage raɗaɗin rayuwa
A wata takarda da sakataren yaɗa labaran mataimakin gwamnan jihar Yobe, Hussaini Mai Sule ya fitar, ya ce, Gwamnan ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Idi Barde Gubana (Wazirin Fune) ya godewa hafsan sojojin bisa wannan ziyarar tare da nuna jin daɗinsa da ƙoƙarin jami’an tsaro na yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka a jihar. Ya yi nuni da cewa sojoji sun yi ƙoƙari sosai wajen dawo da zaman lafiya a jihar Yobe da sauran sassan yankin Arewa maso Gabas.
Ya kuma yi ƙira ga jami’an tsaro da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ganin sun dawo da cikakken zaman lafiya domin jama’a su yi aiki a gonakinsu ba tare da wata fargaba ba.
Tun da farko da yake jawabi yayin ziyarar, babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar TA Lagbaja, ya bayyana cewa ya je jihar ne domin rangadin rundunonin soji da runduna a yankin Arewa maso Gabas.
Ya ce a matsayinsa na babban hafsan soji yana sane da ƙalubalen da ake fuskanta a kewayen Damasak da Gaidam da sauran wuraren da ‘yan ta’adda ke ci gaba da yin barazana. Babban hafsan sojojin ya jaddada cewa yana ƙoƙarin shawo kan matsalar cikin gaggawa.
Lagbaja ya yabawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe bisa gagarumin goyon bayan da aka baiwa sojojin Najeriya.
[…] KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya yaba wa jami’an tsaro wajen ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a jihar […]