Gwamnan Yobe ya rattaɓa hannu kan zartar da hukumar Hisbah da YITDA a jihar

0
260

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON, ya rattaɓa hannu na zartar da wasu ƙudirori biyu na kafa Hukumar Hisbah, da Hukumar Bunkasa Fasaha ta Jihar Yobe (YITDA) a matsayin doka a faɗin jihar.

A wata takardar manema labarai da Mamman Mohammed, babban darakta na harkokin ‘yan jarida da watsa abarai na gwamnan jihar Yobe ya fitar, ya ce, dokar Hukumar Hisbah ita ce ta sanya ido kan aiwatar da Shari’a tare da hana sauran munanan ɗabi’u a cikin jihar.

Hakazalika dokar hukumar bunƙasa fasahar sadarwa ta jihar Yobe ita ce haɗa kai da da cibiyoyi wajen ba da horo da horar da matasa a fannin fasahar sadarwa a jihar.

Dokokin biyu da majalisar dokokin jihar Yobe ta samar da kuma mai girma gwamna Buni, sun fara aiki ne a ranar 6 ga Oktoba, 2023.

Leave a Reply