Gwamnan Yobe ya je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mawallafin jaridar Neptune Prime

0
185

Daga Ibraheem El-Tafsser

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mawallafin jaridar Neptune Prime Dakta Hassan Gimba, a gidansu da ke garin Potiskum jihar Yobe.

Gwamnan Yobe, wanda mataimakinsa Alhaji Idi Barde Gubana (Wazirin Fune) ya wakilce shi, ya bayyana rashin Hajiya Hafsat Ahmed, a matsayin babban rashi, ba ga ‘ya’yanta kaɗai ba, ga dukkan al’ummar musulmi.

KU KUMA KARANTA: Mahaifiyar Mawallafin Neptune Prime, Hassan Gimba, ta rasu tana da shekara 85

Hajiya Hafsat wadda ta rasu ranar Talata, ta rasu tana da shekaru 85. Ta bar ‘ya’ya tara da jikoki da ‘ya’yan jikoki 77.

Ya yi addu’ar Allah ya jiƙanta da rahama, ya gafarta mata.

Leave a Reply