Connect with us

Labarai

Gwamnan Yobe ya je ta’aziyyar rasuwar Hajiya Aisha Mangal

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni CON, ya je Katsina yau domin yin ta’aziyya ga Alhaji Ɗahiru Barau Mangal, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Aisha Mangal, wadda ta rasu a ƙarshen makon da ya gabata.

Gwamnan ya bayyana rasuwar marigayiyar Hajiya A’isha a matsayin babban rashi, uwa kuma mai taimakon jama’a da ‘yan uwa da jihar Katsina da sauran al’umma za su yi kewarta.

‘Ina roƙon Allah (T) ya gafarta mata kura-kuranta, ya kuma sa ta huta, ya sa Aljannatul Firdausi.

“Hakazalika ina addu’ar Allah ya jajantawa iyalan Barau Mangal, ya kuma basu ikon jure wannan babban rashi” Gwamna Buni ya yi addu’a.

Alhaji Ɗahiru Barau Mangal, hamshaƙin attajirin nan na Katsina, ya kasance yana da alaƙa da gwamnatin Buni da ci gaban jihar Yobe.

KU KUMA KARANTA: Buhari, Tinubu sun miƙa ta’aziyyar rasuwar matar Aminu Ɗantata

Ya bayar da gudumawa sosai a wajen ƙaddamar da asusun neman ilimi na jihar Yobe domin tallafawa ci gaban ilimi a jihar Yobe.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

'Yansanda

‘Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

Published

on

Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

‘Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta sanar da cafke wasu mutum biyu bisa zargin hannu a garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara.

Mai magana da yawun rundunar a Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce “muna tsare da mutum biyu kan lamarin, muna ci gaba da bincike.”

Tun farko, Kwamishinan tsaro na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu ya ce an sace dattijuwar ce a daren Juma’a a ƙauyen Kahutu da ke Karamar Hukumar Ɗanja.

Mu’azu ya ce waɗanda suka sace matar sun yi hakan ta hanyar bi ta bayan gida, inda suka sace ta ba tare da jami’an da ke tsaron gidan sun sani ba.

Ya kuma bayyana cewa tuni aka tura jami’an tsaro waɗanda suka bazama cikin dazuka domin bin sawun ’yan bindigar.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar mawaƙi Rarara

Neptune Prime Hausa ta ruwaito shaidu a kauyen sun ce da misalin karfe daya na dare ne dandazon ’yan bindiga suka kutsa gidan dattijuwar suka yi awon gaba da ita.

“A kafa suka zo, ba su yi harbi ba a lokacin da suka ka yi awon gaba da ita cikin ’yan mintoci.

“Dattijuwar ba ta bijire musu ba a lokacin da suka memi ta biyo su.

“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, amma mahaifiyar Rarara kaɗai suka ɗauka.

“Babu wani yunƙuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda bindigogin da suke ɗauke da su,” in ji wani mazaunin ƙauyen na Kahutu.
Ya ce, “Watakila maharan sun bar baburansu ne daga nesa suka tako zuwa cikin ƙauyen a kafa.

“Muna rokon Allah Ya kuɓutar da ita cikin koshin lafiya domin tana taimaka mana sosai a wannan ƙauyen.

“Danta Rarara mai yawan taimakon al’umma ne, kuma ya kawo mana abubuwan ci gaba sosai a garinmu,” in ji shi.

Continue Reading

Labarai

ECOWAS na buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don kafa rundunar tsaro – Badaru

Published

on

ECOWAS na buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don kafa rundunar tsaro - Badaru

ECOWAS na buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don kafa rundunar tsaro – Badaru

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS tana buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don samar da ƙaƙƙarfar rundunar tsaro da za ta yi yaƙi da ta’addanci, a cewar ɗaya daga cikin zaɓuka biyun da hukumomin tsaro na ƙasashen yankin ke duba yiwuwarsu a taron da suka yi a jiya Alhamis.

Ministocin Tsaro da na Kuɗi na Ƙasashen ECOWAS sun yi taron a Abuja, babban birnin Najeriya, inda suka tattauna kan yanke shawarar yawan dakarun da kuma yawan kuɗaɗen da ake buƙata don samar da ita.

Afirka ta Yamma na fama da matsalolin juyin mulki, lamarin da yake zama matsala ga tsarin siyasa da jawo rarrabuwar kai tsakanin ƙasashen yankin.

KU KUMA KARANTA: Masana sun yi ƙira da a yi sabbin sauye-sauye ECOWAS

A watan Janairu, shugabannin mulkin soji na Nijar da Burkina Faso da Mali sun yanke shawarar ficewa daga ƙungiyar mai mambobin ƙasashe 15.

Ministan Tsaron Najeriya ya shaida wa taron cewa akwai zaɓi biyu a samar da rundunar yankin: Daya za a kashe dala biliyan 2.6 duk shekara a kan runduna mai dakaru 5,000, dayan kuma za a kashe dala miliyan 481 a dakaru 1,500
“Waɗannan alkaluma sun nuna muhimmancin aikin da ke gabanmu,” in ji Badaru.
“Don haka ya zama wajibi mu yi nazari sosai kan zabin duba da irin kalubalen da yankinmu ke fuskanta a halin yanzu da kuma matsalolin kudi da kasashe mambobinmu ke fuskanta.”

Tun a shekarar 2020, sojoji a kasashen uku suka yi juyin mulki suna zargin shugabannin farar hula da ƙyale masu da’awar jihadi su samu galaba.

Da hawansu kan mulki, sojojin sun yi watsi da yarjejeniyoyin tsaro da aka ƙulla da sojojin Amurka da Faransa da kuma na Majalisar Dinkin Duniya tare da gayyatar Rasha da su maye gurbinsu.

Ministan Tsaron Nijeriya ya kara da cewa ba za a yi amfani da rundunar yankin wajen ɗaukar mataki a kan juyin mulkin ba, illa kawai yaƙi da ta’addanci. Ana sa ran kowace ƙasa mamba za ta ba da gudunmawar wani kaso, in ji shi.

Shugaban hukumar ECOWAS Omar Touray ya ce ba za a cire mambobin da aka dakatar daga cikin rundunar yankin ba.

“An yi imanin ba za mu iya yaki da ta’addanci mu kadai idan har wasu ba su shiga ba,” in ji Touray.

“Ko da yake ana iya dakatar da wasu kasashe amma ya kamata a bar su su shiga tarukan da suka shafi tsaro, shi ya sa muka gayyaci dukkan kasashe mambobi 15 da su halarci wannan muhimmin taro.”

Continue Reading

Labarai

Saudiyya na son fara shigar da naman shanu da waken suya ƙasarta daga Najeriya

Published

on

Saudiyya na son fara shigar da naman shanu da waken suya ƙasarta daga Najeriya

Saudiyya na son fara shigar da naman shanu da waken suya ƙasarta daga Najeriya

Ministan Harkokin Noma na Najeriya Mohammad Abubakar ya ce Saudiyya ta nuna sha’awar fara shigar da ton 200,000 na naman shanu da ton miliyan ɗaya na waken suya cikin ƙasarta duk shekara daga Najeriya.

Minista Mohammed ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja cewa Saudiyya ta nuna sha’awar hakan ne bayan da Ministanta na Harkokin Noma ya ziyarci Najeriya tare da yin wasu taruka da ‘yan kasuwa a fannonin noma.

“Nuna sha’awar tasu kan wannan batu ke da wuya sai muka fitar da wani tsari da za mu iya samar da yawan abin da suke so da kuma biya musu buƙatarsu,” a cewar Ministan Harkokin Noman na Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Masu sana’ar sayar da tumatur sun yi barazanar daina kai wa jihar Legas

Ya ƙara da cewa dama Najeriya na neman abokan hulɗa na kasuwanci don samun kuɗaɗen ƙasashen waje bayan da ta sha fama da ƙarancin dalar Amurka, lamarin da ya yi mummunar illa kan tattalin arzikinta da kuma rage darajar kudin ƙasar na Naira sosai.

Najeriya ta daɗe tana son raba ƙafa kan harkokin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, maimakon fitar da ɗanyen man fetur kawai, wanda a yanzu fitar da shi shi kaɗai ba ya iya riƙe tattalin arzikinta sosai.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like