Daga Ibraheem El-Tafseer
Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni (Chiroman Gujba) a yau Laraba 20-Satumba-2023 ya jagoranci taron tsaro na ƙasa da aka saba gudanarwa a gidan gwamnati dake Damaturu, tare da halartar shugabannin hukumomin tsaro.
Gwamnan, ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Idi Barde Gubana (Wazirin Fune) wanda ya bayyana cewa ya dace a tattauna kan matsalar tsaro a jihar domin tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar jihar ta hanyar kare rayuka da dukiyoyinsu.
Ya yaba wa hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya, da doka da oda a jihar.
Taron ya kuma yaba da ƙoƙarin sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma na magance rikice-rikice a tsakanin yankunansu.
Jim kaɗan bayan kammala taron kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe Ahmad Garba ya bayyana wa ‘yan jarida sakamakon taron inda ya tabbatar da cewa jami’an tsaro za su ƙara sanya ido da kuma sintiri a yankunansu domin daƙile matsalar hare-haren makiyaya da garkuwa da mutane da fashi da makami da fyade a jihar.
KU KUMA KARANTA: Gwamna Yobe ya ba da tallafin kuɗi a mutane 1000 waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa
Ya kuma yi ƙira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya tare da bayar da bayanan da suka dace domin ci gaba da samun zaman lafiya a jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, babban lauyan gwamnati da kwamishinan shari’a da mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro sun halarci taron.
Sauran shugabannin hukumomin tsaro da suka halarci taron sun haɗa da, sashe na 2 Commandant Operation Lafiya Dole, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, daraktan tsaro kwamandan tsaro na Civil Defence Corp, Commandant Nigeria Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) da Daraktan tsaro na ofishin gidan gwamnati da sauran jami’an tsaro.