Gwamnan Yobe ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina saboda halin rashin ɗa’a

0
105
Gwamnan Yobe ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina saboda halin rashin ɗa'a

Gwamnan Yobe ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina saboda halin rashin ɗa’a

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON, ya amince da dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina, Idrissa Mai Bukar Machina nan take bisa aikata laifin rashin ɗa’a da kuma rashin biyayya.

A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labarai na sakataren gwamnatin jihar, Shuaibu Abdullahi, ta ce gwamna Mai Mala Buni a bisa aiwatar da ikon da sashe na 2 na dokar ƙananan hukumomi (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima) 2019 ya ba shi, ya amince da dokar dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina, Idrissa Mai Bukar Machina da aka yi nan take saboda halin rashin ɗa’a da kuma rashin biyayya.

KU KUMA KARANTA: ’Yan sanda za su tantance ’yan banga a Yobe

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa Gwamna Mai Mala Buni ya kuma umarci shugaban da aka dakatar da ya miƙa al’amuran ƙaramar hukumar ga mataimakin shugaban.

Leave a Reply