Gwamnan Yobe ya bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura

0
31
Gwamnan Yobe ya bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura

Gwamnan Yobe ya bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura don kyautata harkar tsaro a jihar.

Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkar tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya) ne, ya miƙa baburan ga ’yan bangar.

A lokacin, ya bayyana cewa wannan tallafin yana daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Abdulsalam, ya ce wannan ba shi ne karon farko da gwamnati ke tallafa wa ’yan banga da kayan aiki ba.

KU KUMA KARANTA: Ana buƙatar fiye da matakin Soja wajen samar da tsaro a Najeriya ; Babban Hafsan Tsaro

Ya ce ko a baya gwamnatin ta ba su irin wannan tallafi don su samu damar gudanar da ayyukansu cikin sauƙi da kwanciyar hankali.

Ya ce tsarin ya nuna ƙudirin gwamnatin na inganta tsaro da kuma tallafawa masu sa-kai don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.

Leave a Reply