Gwamnan Yobe ya amince da ɗaukar ma’aikatan jinya 158, da ba da alawus ga ɗalibai 393

0
275

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni CON, ya amince da ɗaukar ma’aikata 158 da suka kammala karatun aikin jinya a Kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma ta Shehu Sule da ke birnin Damaturu.

A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na Gwamnan jihar Yobe, Mamman Mohammed ya fitar, ya ce waɗanda suka ci gajiyar shirin, sune waɗanda suka kammala karatun aikin jinya a kwalejin.

Hakazalika, Gwamna Buni ya amince da biyan Naira 10,000 alawus-alawus na kowane wata ga ɗalibai 393 ‘yan asalin jihar Yobe, waɗanda suke gudanar da karatun Diploma a kwalejin aikin jinya ta Shehu Sule.

Amincewar ta nuna cewa 67 daga cikin ɗaliban da suka amfana suma suna da haƙƙin yin aiki a jihar na tsawon watanni 11.

Har ila yau, ya bayyana cewa sabbin ɗalibai 326 ‘yan asalin jihar Yobe da ke gudanar da Basic Midwifery da Diploma a fannin aikin jinya, za su fara cin gajiyar alawus-alawus na Naira 10,000 da aka amince da su duk wata.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya rattaɓa hannu kan zartar da hukumar Hisbah da YITDA a jihar

Gwamna Buni ya buƙaci sabbin ma’aikatan lafiya da aka ɗauka aiki da su jajirce wajen yi wa al’umma hidima.

Ya buƙace su da su sanya hannu a cikin shirin sake fasalin gwamnatin jihar domin samar da ingantattun ayyukan jinya, da sauƙi ga jama’a.

Gwamnan ya kuma yi ƙira ga ɗaliban da su yi karatun ta natsu domin tabbatar da jarin da gwamnati ta saka musu.

Leave a Reply