Gwamnan Sakkwato ya warewa kowane masallacin juma’a Naira dubu 300 duk wata, za ana bawa limamai da ladanai alawus 

0
182
Gwamnan Sakkwato ya warewa kowane masallacin juma'a Naira dubu 300 duk wata, za ana bawa limamai da ladanai alawus 
Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu

Gwamnan Sakkwato ya warewa kowane masallacin juma’a Naira dubu 300 duk wata, za ana bawa limamai da ladanai alawus

Gwamnatin jihar Sokota ta ce za ta fara ware wa masallatan Juma’a na jihar wasu kuɗaɗe duk wata domin gudanar da ayyukansu, sannan ta ce tana ware wa limaman masallatan da na’ibansu da ladanai alawus duk wata.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin jihar, Abubakar Bawa ya fitar, inda ya ce gwmnatin ta ɗauki wannan matakin ne domin haɓaka karatun Alƙur’ani da ilimin addini a tsakanin yaran jihar masu tasowa.

Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana haka a ranar Asabar a wajen yayen ɗalibai 111 da suka haddace Ƙur’ani a makarantar gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi da ke Sokoto, inda ya ƙara da

 cewa alawus ɗin zai taimaka wajen ba malaman addinin damar nazari da ci gaba da karantar da addini.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Sakkwato ya karɓe ikon naɗa sarakuna da Hakimai daga hannun sarkin musulmi

“Mun bayar da kwangilar sabunta masallatai 65 na Juma’a, kuma tuni an kammala guda 25, waɗanda a ciki mun buɗe guda 15 zuwa yanzu.

“Haka kuma mun kasafta ware wa masallatan na Juma’a kuɗi tsakanin naira 300,000 zuwa 500,000, ya gandanta. Sannan ga biyan limamai da na’ibai da ladanai na masallatan alawus suma domin samun sauƙin gudanar da ayyukansu,” in ji shi.

Gwamnan ya ce kula da harkokin addinin musulunci na cikin manufofi 9 na gwamatinsa, “kuma shi ne mai matsayi na biyu bayan tsaro.”

Leave a Reply