No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin Sakkwato ta sallami hakimai 15 bisa zargin su da taimakawa rashin tsaro, satar filaye da sauran laifuka.

An sallami hakimai 9 daga mukamansu bisa zargin su da rashin biyayya da taimakon rashin tsaro da satar filaye da kuma karkatar da dukiyar jama’a da rashin da’a.

Waɗanda aka sallama su haɗa da hakiman Uguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, llela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, da kuma Hakimin Gyawa.

Gwamnatin jihar ta kuma sauƙe wasu hakimai shida da tsohuwar gwamnatin jihar ta naɗa.

KU KUMA KARANTA: Masarautar Bauchi ta tuɓe rawanin sarakai 6

Abubakar Bawa, Sakataren yaɗa labarai na Gwamna Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa an sauke hakiman shida ne saboda yadda aka naɗa su bisa ga ƙa’ida da kuma ƙin amincewa da mutanensu suka yi.

Su haɗa da hakimin Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, Bunun Gongono, Sarkin Kudun ’Yar Tsakkuwa, da kuma  Sarkin Tambuwal da Sarkin Yamman Torankavwa.

Bawa ya ƙara da cewa “An yaba da ƙararrakin da suka shafi Hakiman Isa, Kuchi, Kilgori da Gagi don ci gaba da bincike.”

Sai dai Sarkin Yaƙin Binji, babban mai ba da shawara a Majalisar Suktanate an mayar da shi Nabunkari yayin da Hakimin Sabon Birni ya kai Gatawa.

Bawa ya lura cewa, an bar wasu hakimai bakwai a kan kujerunsu da suka hada da Alhaji Aliyu Abubakar III (Shugaban Sokoto); Alhaji Ibrahim Dauki Maccido (Barayar Zaki); Abubakar Salame (Sarkin Arewan Salame) da Aminu Bello (Sarkin Yamman Balle).

Sauran su ne Mahmoud Yabo (Sarkin Gabas Dandin Mahe); Muntari Tukur Ambarura (Sarkin Gabas Ambarura) da Malam Isa Rarah (Sarkin Gabas Rarah).

Hakazalika, Hakiman Tsaki da Asare suma an rike su yayin da aka mayar da Abdulkadir Mujeli a matsayin Sarkin Rafin Gumbi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...