Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun da muƙarrabansa sun tsallake rijiya da baya a wani hatsarin jirgin sama bayan jirgin da suka shiga, ya kama wuta daf da tashinsa.
Wani rahoto da jaridar Leadership ta fitar, ya nuna cewa, a ranar Talata, 5 ga Satumba, 2023, wani Bombadier Global Express 6000, mallakin hamshaƙin attajirin ɗan kasuwa, Cif Adedeji Adeleke, ya kama wuta a tashar tashin jirgin sama na Murtala Mohammed International Airport (MMIA) a Legas.
Cif Adeleke shi ne mahaifin mawaƙi, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, kuma ɗan uwa ne ga gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke.
KU KUMA KARANTA: Jirgin ƙasa ya tsallake rijiya da baya a hanyar Abuja zuwa Kaduna (Bidiyo)
Lamarin ya faru ne a sashin gida na filin jirgin da misalin ƙarfe tara na safe a daidai lokacin da jirgin ke shirin tashi daga Legas zuwa Abuja.
Rahoton ya bayyana cewa jirgin da Gwamna Adeleke da muƙarrabansa da ke cikin jirgin, an tuƙa shi ne zuwa ƙarshen titin jirgin daf da tashinsa, sai aka ji ƙarar fashewar wani abu daga injin jirgin.
Rahoton ya ƙara da cewa, kafin tashin jirgin, an ajiye jirgin ne a babban ma’aikatar sufurin jiragen sama na Executive Jet.
Sam Iwuajoku, babban jami’in gudanarwa (CEO), Executive Jets, waɗanda suka mallaki hangar da aka ajiye jirgin mai zaman kansa, ya bayyana cewa jirgin na Cif Adeleke ya samu Lalacewar Abun Wuta (FOD) wanda ya sa jirgin ya yi zafi sosai, wanda ya haifar da tashin hankali fashewar.
“Lokacin da aka tashi, injin yana da zafi sosai kuma ya faru ne sakamakon gijen tsuntsu a ɗaya daga cikin injinan jirgin. Ya faru ne lokacin da aka ajiye jirgin ba a rufe shi yadda ya kamata ba, tsuntsaye za su gina gida kuma duk abin da suka kawo cikin injin jirgin zai iya haifar da zafi mai tsanani” Sam Iwuajoku ya shaida wa jaridar.
Ya faru da ɗaya daga cikin jirgin sama na a 2021, dole ne muka cire injin kuma muka kai injin ƙasar Jamus tsawon watanni 14 ana gyaransa. Don haka, abu ne gama gari a Afirka saboda muna da tsuntsaye a kusa, ”in ji shi.