Gwamnan Neja ya yi afuwa ga fursunoni 80, saboda ranar dimokuraɗiyya

0
400

Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya yi afuwa ga wasu fursunoni 80 da ke gidajen gyaran hali daban-daban a faɗin jihar.

Gwamnan ya kuma amince da a biya tarar da aka musu cikin gaggawa, domin baiwa fursunonin damar komawa cikin iyalansu.

A wata sanarwa da Abubakar Usman, sakataren gwamnatin jihar (SSG), ya fitar a Minna a ranar Litinin, ya ce an gudanar da bikin ne domin murnar zagayowar ranar dimokuraɗiyya ta 2023.

Ya bayyana cewa sakin fursunonin ya yi daidai da ikon jinƙai da tsarin mulki ya baiwa gwamna.

Usman ya ce majalisar ba da shawara kan jinƙai ta jihar ta ba da shawarar a saki fursunonin 80 saboda tsufa, rashin lafiya da kuma kyawawan halaye.

KU KUMA KARANTA: Fursunoni 3,298 ke fuskantar hukuncin kisa a Najeriya – Hukumar NCoS

Usman ya yi ƙira ga fursunonin da su yi amfani da damar da suke da su wajen yin sana’o’i masu amfani tare da yin watsi da duk wani abu da zai kai su gidan yari.

Ya kuma gargaɗe su da su kasance masu bin doka da oda da gudanar da ayyukan da suka dace ta hanyar amfani da hanyoyi daban-daban na ƙarfafawa.

SSG ta yi ƙira ga al’ummar jihar da su yi amfani da wannan lokacin wajen yin tunani kan rawar da suke takawa wajen samar da zaman lafiya da goyon bayan gudanar da shugabanci na gari.

Ya kuma umarce su da su tallafawa shirye-shirye da manufofin gwamnati da aka tsara don kawo ci gaba cikin sauri a jihar.

Usman ya tabbatar da cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa an samu rabon dimokuraɗiyya a dukkan lungu da saƙo na jihar nan.

Ya kuma buƙaci al’ummar jihar da kada su bari rashin jin daɗi ya maye gurbin fata, ya ƙara da cewa ya kamata su sabunta alƙawarin ƙarfafa hukumomin dimokaraɗiyya da nuna haƙuri, kishin ƙasa da kuma ɗa’a.

SSG ya ce gwamnati ta damu matuƙa game da ƙalubalen tsaro a jihar kuma ta shirya tsaf domin tunkarar lamarin.

Leave a Reply