Gwamnan jihar Neja Umaru Bago ya rusa ofishin ‘yan sanda na Chanchaga dake Minna.
A cewar wata sanarwa da mai bawa gwamnan shawara na musamman kan harkokin sadarwa na zamani, Abdullberqy Ebbo ya fitar, ta ce an gina ofishin ‘yan sanda ba bisa ƙa’ida ba a kan wani babban bututun ruwa.
Idan dai za a iya tunawa, gwamnan a yayin jawabinsa na ƙaddamar da aikin, ya sha alwashin rusa ofishin ‘yan sanda saboda kawo cikas ga samar da ruwan sha a babban birnin jihar.
Ebbo ya ce ofishin ‘yan sandan da ke daura da hukumar ruwa ta jihar an gina shi ne ba bisa ƙa’ida ba saboda rashin mutunta ƙa’idojin tsare-tsare.
“Ginin ba shi da izinin da ake buƙata kuma yana zaune a kan babban bututun ruwa.
KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC ta gurfanar da ma’aikatan bankin UBA biyu, bisa laifin satar naira miliyan 20
“Gwamna Mohammed Umaru Bago, wanda ya sanya samar da ruwan sha a matsayin wani ɓangare na ayyukansa, zai yi duk abin da zai iya yi a matsayinsa na gwamna wajen samar da ruwan sha ga al’ummarsa,” inji sanarwar.
A halin da ake ciki, gwamnati ta kuma gargaɗi ƙungiyoyi, cibiyoyi, da ɗaiɗaikun jama’a da su nemi izini daga hukumomin da abin ya shafa kafin kafa wani gini.
Ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar ƙwararan matakai kan duk wanda aka samu yana son rashin bin doka da oda a jihar.
Hakazalika, gwamnan ya kuma bayar da umarnin soke takardar shaidar zama mai suna C of O, tare da rushe wani gidan mai na Ashrab Energy Limited nan take. Gwamnan ya ba da umarnin ne a lokacin da ya ziyarci gidan mai da ke Ketaren Gwari, Minna.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Bologi Ibrahim, ya fitar ta ce tsarin ya saɓawa doka kuma yana barazana ga rayuwar al’ummar yankin.
Ya kuma ce mahukuntan gidan man sun yi watsi da umarnin da ya ba su na dakatar da aikin da ake yi.
“Mun samu rahoton tsarin da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, kuma na nemi hukumar raya birane da ta dakatar da su daga aiki amma sun ci gaba, don haka mun soke takardar C of O daga yau, kuma za mu sanya masa alama don rushewa.