Gwamnan Neja bai yi mana adalci ba - Hukumar Alhazai

Gwamnan Neja bai yi mana adalci ba – Hukumar Alhazai

Gwamnan Neja bai yi mana adalci ba – Hukumar Alhazai

Hukumar aikin Hajji ta ƙasar watau, NAHCON ta mayar da martani kan zargin da gwamnan jihar Neja ya yi mata na rashin shirya ingantaccen aikin Hajji a bana.

Hukumar ta ce gwamnan bai yi mata adalci ba idan aka yi la’akari da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar naira da kuma kasancewarta mai sa ido ce ba mai ɗaukar ɗawainiyar mahajjata ba.

Gwamna Umaru Bago ya yi zarge-zargen a Saudiyya, a wani taron manema labarai.

Mai magana da yawun hukumar, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta ce ƙasar Saudiyya ba ta hulɗa da jihohi a kan harkar aikin Hajji, illa ƙasashe kawai.

KU KUMA KARANTA: A rushe NAHCON ba ta da amfani — Gwamnan Neja

‘Ba zai yiwu a ce jihar Neja ta je Saudiyya don yin yarjejeniya kan alhazanta ba. Idan gwamnan ya ce a ɗauki ayyukan a mayar da su kan jihohi akwai ayar tambaya a kai,” in ji Fatima Sanda.

Ta ce ” Sa ido ne kawai NAHCON ke yi ba ita take kwashe alhazai zuwa Saudiyya ba. Jiragen sama ne ke da alhakin haka.

Dangane da zargin da gwamnan na Neja ya yi kan yanayin lafiyar mahajjata kuwa, Hajiya Fatima ta ce ba abin da ya haɗa da NAHCON da wannan saboda alhakin ya rataya kan jihohi, inda ta ce haka ne ma yake sa wani lokaci ake samun mata masu ciki da ke tafiya zuwa aikin Hajji.

“Muna sonmu tunatrawa gwamna Bago cewa hukumomin jihohi ne ke zaɓar waɗanda za su ciyar da alhazansu da kuma irin abincin da suke so ba wai hukumar mu ba, don haka idan suka zauna da yunwa ba laifin mu bane,” kamar yadda Fatima Usara ta shaida wa BBC.
Ta kuma yi watsi da batun cewa NAHCON ta gaza a ayyukanta na gudanar da aikin Hajji.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *