No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya rasa ƙaninsa Labaran Sule.

Jaridar DAILY NIGERIAN  ta ruwaito cewa ɗan’uwan ​​gwamnan ya rasu ne a safiyar ranar Asabar. Mutuwar Labaran na zuwa ne ‘yan watanni kaɗan bayan da gwamnan ya rasa ɗansa, Hassan Sule, ranar 27 ga watan Janairu, yana da shekaru 36 bayan gajeriyar rashin lafiya.

KU KUMA KARANTA: An yi jana’izar babban ɗan Gwamnan Nasarawa da Allah Ya yiwa rasuwa

Da yake tabbatar da rasuwar ɗan’uwan ​​gwamnan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai taimaka wa gwamnan, Musa Barau, ya ce za a yi sallar jana’izar marigayin ne a fadar Mai martaba sarkin Gudi da ke ƙaramar hukumar Akwanga ranar Asabar.

“A cikin baƙin ciki ne muka sanar da rasuwar ƙanin Gwamnan Jihar Nasarawa Labaran Sule.

“Za a yi jana’izar marigayin ne a fadar Sarkin Gudi, a ƙaramar hukumar Akwanga. Allah ya jikansa da rahama a Aljannatul Firdausi, Ameen ya rabbi.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...