Gwamnan Katsina ya umarci a binciki malamin da yayi lalata da ɗalibarsa a Ɗandume

0
194

Gwamna Raɗɗa ya umarci a binciki malamin da yayi lalata da ɗalibarsa a Ɗandume

Alfijir labarai ta rawaito gwamnatin jihar Katsina ta bada umarnin yin bincike game da malamin makarantar sakandire da ake zargin yayi lalata da ɗalibar sa a ƙaramar hukumar Ɗandume dake jihar Katsina.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da ke ɗauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai dake ofishin sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Aliyu Yar’adua, a ranar Juma’a ya sanyawa hannu a madadin fadar gwamnatin jihar.

KU KUMA KARANTA: Makaho ya damfari wata mata naira miliyan 19, ya yi lalata da ‘yarta da jikarta

Sanarwar tace, gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, ya samu rahoto da ake zargin wani malamin makarantar sakandare mai suna Lawal Ibrahim, da ake zargin yayi lalata da wata ɗalibarsa.

Da jin hakan ba da jimawa ba, gwamnan jihar ya umurci kwamishinar ma’aikatar ilmin firamare da na sakandare ta jihar Katsina da su gaggauta dakatar da malamin mai suna Lawal Ibrahim, sannan a gudanar da bincike a kan lamarin inji sanarwar.

Kazalika, gwamnan ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina da ya binciki lamarin, tare da bincikar baturen ‘yan sandan (DPO) na ƙaramar hukumar Dandume wanda ake zargi da karɓar na goro domin lalata maganar game da batun malamin makarantar.

Leave a Reply