Gwamnan Katsina ya ceto wanda ’yan ta’adda suka sace

Gwamnan Katsina, Dikko Raddah, ya jagoranci fatattakar ’yan bidiga a ƙauyen Zakka a ƙaramar hukumar Safana ta jihar.

Gwamnan ya jagoranci jami’an tsaro haɗin gwiwa wajen ceto wani matashi da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi.

Dikko Radda ya jagoranci kai ɗaukin ne a lokacin da ya je ƙaramar hukumar ƙaddamar da shirin tallafi na mataimakin shugaban majalisar jihar,  Abduljalal Runka.

Sakataren yaɗa labaran gwamna, Kaula Mohammed, ya ce kafin ƙaddamar da tallafin ne jami’an tsaro suka samu ƙiran gagawa cewa ’yan ta’adda sun kai hari ƙauyen Zakka.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Kaula na cewa, nan take gwamnan ya dakatar da shirin, shige gaba aka fatattaki ’yan bindigar, aka ceto matashin.

Daga nan gwamnan ya ba da umarnin kai mutumin asibiti domin kula da shi, saboda harbin sa da aka yi a kafa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *