Daga Ibraheem El-Tafseer
Gwamnan jihar Katsina Alhaji Dikko Umaru Raɗɗa, a ranar Talata 22 Agusta, 2023, ya ƙaddamar da kwamiti mai mutune 20 da za su taimaka wajen tsara taswira mai inganci da za a yi amfani da ita don ƙara haɓaka ci gaban jihar Katsina.
Kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin mataimakin Gwamnan jihar Hon. Faruq Lawal Jobe. Sauran membobin kwamitin sun haɗa da: Sakataren gwamnatin jihar Katsina, kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziƙi, kwamishinan Kuɗi, kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, kwamishinan raya karkara, kwamishinan Ilimin na firamare da na Sakandare, da kuma na kwamishinan ilimi mai zurfi da horar da sana’o’in hannu.
Sauran sun haɗa da wakilan Masarautar Katsina da Daura, Majalisar Malamai ta Jiha, ƙungiyoyin fararen hula da ƙungiyoyin ƙwadago da Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha da dai sauransu.
Da yake bayyana nauyin da aka ɗora wa kwamitin, Gwamna Raɗɗa, ya ce kwamitin na da hurumin sake duba daftarin shirin raya jihar Katsina, bayan nazarin tsare-tsaren ci gaban jihohin Jigawa da Kaduna da kuma Kano da ke maƙwabtaka, da nufin ɗaukar wasu kyawawan ayyuka da tsare-tsaren da suka dace da hakan zai ƙara ƙarfafa ingantaccen tsarin ci gaban jiha.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Katsina za ta kafa hukumar Zakka – Raɗɗa
Gwamnan, ya ce kwamitin zai kuma tattara tare da nazari da kuma haɗa buƙatu na al’umma waɗanda suka dace da dabarun shirin ci gaban Katsina, tare da haɗa manufofin da suka dace daga cikin daidaiton rahoton tsarin ci gaban jihar.
Raɗɗa, ya taya membobin kwamitin murna, ya yi fatar za su kammala aikinsu, cikin lokacin da aka ƙayyade musu, su miƙa rahoton ga gwamnatin jihar Katsina.