No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Raɗɗa ya naɗa Ahmed Dangiwa a matsayin sakataren gwamnatin jihar.

A wata sanarwa da shi da kansa ya sanya wa hannu a ranar Litinin, gwamnan ya kuma naɗa Jabiru Tsauri a matsayin shugaban ma’aikatan jihar da Mukhtar Saulawa a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan, sai Abdullahi Turaji a matsayin babban Sakataren Gwamnan.

Sauran naɗin da Gwamna Raɗɗa ya amince da su sun haɗa da Maiwada Danmallam a matsayin babban Darakta na yaɗa labarai, Ibrahim Kaula Mohammed a matsayin babban sakataren yaɗa labarai, Miqdad Isah a matsayin babban mataimaki na musamman (Digital Media) da Abubakar Jikamshi a matsayin Babban Mataimaki na Musamman (Print and Electronic Media).

KU KUMA KARANTA: Sabon Gwamnan Kano Abba Gida-Gida, ya naɗa shugaban ma’aikata da sakataren gwamnati

Gwamnan ya kuma naɗa Bishir Maikano a matsayin babban mataimaki na musamman (Protocol) na Gwamnan.

Sauran naɗin sun haɗa da Hassan Danhaire a matsayin babban mataimaki na musamman (Special Services) mataimakin gwamna da Ahmed Rabiu a matsayin mai ɗaukar hoto na gwamna.

Gwamnan ya taya sabbin waɗanda aka naɗa murna tare da buƙace su da su haɗa kai da shi wajen ganin an dawo da dukiyar jihar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

2 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...