Gwamnan Kano ya tarbi tagwayen da aka haifa a haɗe, bayan an yi aikin raba su a Saudiyya

0
251
Gwamnan Kano ya tarbi tagwayen da aka haifa a haɗe, bayan an yi aikin raba su a Saudiyya
Gwamnan Kano Abba tare da tagwayen bayan sun iso Najeriya

Gwamnan Kano ya tarbi tagwayen da aka haifa a haɗe, bayan an yi aikin raba su a Saudiyya

Tagwayen da aka haifa a nanne da juna, Hassana da Husaina, waɗanda aka yi aikin raba su a Saudiyya sun dawo gida inda aka tarbe su cikin farin ciki a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA).

An tafi da tagwayen zuwa birnin Riyadh a watan Oktoba, 2023, inda aka shafe watanni ana musu cikakkun gwaje-gwajen likitanci.

Likitoci sun gano cewa tagwayen sun hade ne a ƙasan ciki, a ƙugu da kuma a kashin baya, inda su ke yin wasu abubuwa na rayuwa tare, lamarin da ya sa aikin ya zama mai haɗari.

KU KUMA KARANTA: Likitocin ƙasar Saudiyya sun yi nasarar raba tagwaye ‘yan Najeriya da suka haɗe

An gudanar da aikin raba sun a Asibitin Kwararru na Yara na Sarki Abdullah da ke Cibiyar Lafiya ta Sarki Abdulaziz, Riyadh, bisa umarnin Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud, da kuma yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al-Saud.

Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Ahmed Al-Admawi, wanda ya halarci taron tarbar iyalin a filin jirgin sama, ya bayyana nasarar aikin a matsayin shaida ta jajircewar masarautar wajen bayar da agajin jinƙai ga al’umma.

Ya ƙara da cewa aikin da aka yi wa tagwayen ya kasance na 65 cikin jerin nasarorin tiyata da aka gudanar a ƙarƙashin Shirin Raba Tagwayen Saudiyya.

Shi ma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna farin ciki da godiya ga Masarautar Saudiyya bisa wannan gagarumin taimako.

Gwamna Yusuf ya kuma yi alkawarin kula da rayuwar yaran har da ta ilimin su.

Haka zalika mahaifan yaran, cikin kuka sun nuna godiya ga wannan taimako.

Leave a Reply